IQNA

23:38 - November 29, 2016
Lambar Labari: 3480984
Bangaren kasa da kasa, Iran da kwamitin kula da harkokin addinai a kasar Uganda za su hannu kan yarjeniyoyi da suka shafi bunkasa alaka ta addinai da al’adu a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslucni cewa, a jiya Jusua Kitakole shugaban kwamitin kula da harkokin addinai na kasar Uganda, ya gana da Ali Bakhtiyari shugaban ofishin kula da harkokin al’adu na Iran a kasar.

Bangarorin biyu dai sun tattauna kan wasu muhimman lamurra da suka shafi kula alaka ta musamman a bangaren musayar ra’ayoyi ta fuskar addinai da al’adu, da kuma yadda za a kara karfafa wannan bangarea tsakaninsu.

Dukkanin bangarorin biyu sun cimma matsaya akan cewa za arattaba hannu kan yarjejeniya ta fuskar addini da kuma al’adu tasakanin bangarorin biyu nan ba da jimawa ba.

Jami’in na Iran ya bayyana cewa babbar manufarsu a kan hakan ita ce kara fadada hanyoyin tattaunawa a tsakanin mabiya addinai daban-daban, domin a kara samun fahimtar juna da hakan zai kara kawo zaman lafiya atsakanin dukkanin al’ummomin duniya.

Ya ce hakan ya zama wajibi, idan aka yi la’akari da yadda wasu kasashen ska bata wa muslnci suna a duniya a halin yanzu, ta hanyar kirkiro kungiyoyin yan ta’adda da suka da sunan muslunci, inda yanzu da dama daga cikin al’ummomin da ba musulmi ba suke yi wa muslunci wani kallo na daban.

3549767

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: