IQNA

Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki A Najeriya

23:41 - November 29, 2016
Lambar Labari: 3480985
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki karo na 31 tare da halartar makaranta kimanin 300 a birnin Suleja na jahar Niger.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na today.ng cewa, Sani Bello gwamnan jahar Najer ya bayyana cewa, mutane 12 suka zo gasar daga jahohi 25 daga cikin jahohin kasar.

Ya ci gaba da cewa bababr manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce, samar da yanayi na karfafa mutane dangane da karatun kur’ani da kuma bayar da muhimamnci kan lamarin kur’ani a kasar.

Ya ce suna da wani shiri na samnar da sabon tsari a makarantun book a arewacin Najeriya, wanda zai kunshi koyar da ilmomin kur’ani tsarki ga yara daliban makarantu na firamare da kuma sakandare.

Abin tuni a nan dai shi ne wannan shi ne karo na 31 da ake gudanar da wannan gasa akowace shekara a Najeriya, kuma akan zabi jahar da za a gdanar a kowace, gasar za ta ci gaba har zuwa ranar Asabar mai zuwa.

3549814


captcha