IQNA

21:00 - November 30, 2016
Lambar Labari: 3480986
Bangaren kasa da kasa, Iraniyawa mazauna birnin Manila sun gudanar da zaman makon shahadar Imam Rida (AS) a ofishin jakadancin Iran.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, an gudanar da wannan zaman mako ne wanda ya fasra tun daga ranar 28 ga watan safar harzuwa 30 ga wannan wata, inda aka yi makokin wafatin manzon Allah (SAW) da shahadar Imam Hassan Mujtaba (AS) da kuma Imam Ridha (AS).

Taron dai ya gudana ne a karamin ofishin kadancin kasar Iran da ke birnin, inda aka gabatar da jawabai da kuma yin makoki na wadanan darare masu babban sha'ani.

Taron na faraway ne a kowane dare daga kimanin karfe 9.30 har zuwa tsakar dare.

Baya ga Iraniyawa masoya manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka (AS) suna taruwa awannan wuri domin nuna alhini.

3549947

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: