Wannan shiri ya zo ne sakamakon karuwar nuna kyamar musulmi da ake yi a kasar tun bayan da gudanar da zaben shugaban kasar Amurka, wanda Donald Trump ya lashe, wanda kuma daya daga cikin abin da ya yi yakin neman zabe da shi a lokacin, shi ne kyamar musulmi.
Babbar manufar wannan horo ita ce yadda musulmi za su rika wayar da kan jama'a da kuma nuna musu muslunci a aikace, domin su tabbatar da cewa addinin muslunci ba addinin ta'addanci ba ne.
Cibiyar musulmin kasar Canada day ace daga cikin cibiyoyi masu kansu, kuma tana gudanar da ayukanta a kowane lokaci domin kare hakkokin musulmi a kasar, da kuma kokarin bayyana ma mutane hakikin koyarwar addini tav zaman lafiya da fahimtar juna, sabanin abin da al'ummar kasar ke zato kan muslunci.