Haka nan kuma n akas abnagrorin hardar zuwa dukkanin kur'ani da kuma juzui 25, sai kuma 20, da kuma 15, da 10, da kuma 5, sa kuma juzui uku.
Kwamitin alkalan gasar ya kunshi alkalai 6 ne da suka fito daga sssa na kasar, kamar yadda kuma wasu daga cikin manyan jami'an gwamnati da suka hada da Jum'a Dun Haji tsohon ministan kiwon lafiya na kasar, da kuma wasu daga cikin malamai, da kuma wasu daga cikin yan majalisar dokoki da suka hada Abdulwahab Al-sarari duk sun halarci wurin.
A taron kammala wannan gasa an gudanar da karatun kur'ani mai tsarki, daga bisani kuma aka bayar da kyautuka ga wadanda suka fi nuna kwazo a gasar, kafin daga bisani kuma a rufe taron.