Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya
nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nan a yaum Sabi cewa, Ammar Mir Gani minister
mai kula da harkokin addinai a kasar Sudan ya bayyana cewa, sun samu nasarar
kwace wasu kwafin ur'anai kimanin 1875 da aka buga akasar da suke da kura-kurai.
Ya ce wannan kuran yana da hanyar da aka yi amfani da kayan bugun rubutun ne yadda aka tsara su, domin kuwa sau da yawa akan samu irin wannan, amma kuma dole a hana yaduwar irin wannan kwafin kur'anai a tsakanin musulmi.
Ya ci gaba da cewa ma;aikatar ta aike da ma'aikatanta domin tattaro irin wadannan kur'anai da aka buga, inda aka duba masallatai da kuma dakunan karatu, da ma wasu daga cikin wadanda suke ahannun mutane, duk kuwa da cewa har yanzu ana kira ga mutane da su taimaka su dawo da wadanda suke a hannunsu.
Kasar Sudan dai tana daga cikin kasashen da suke buga kur'anai a yankin nahiyar Afirka, wanda kuma dukkanin cibiyoyin da ke buga kur'anai suna samun takardun izinin hakan ne daga manyan cibiyoyin muslunci.