Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na inews880 cewa, Janil Wana wata muuslma ‘yar kasar ta Canada, ta bayyana cewa tana da shiri bayar da furanni daga gobe a tashar jiragen kasa ta Alborta.
Wannan tasha dai tana daga cikin tashsohin jiragen kasa mafi cunkosoa kasar ta Canada, kuma a nan masu kyamar musulunci suke taruwa suna yin kalaman batunci ga masulmi da muslunci da yin zane-zanen batuncia bangaye.
Matar ta ce ta zabi wannan wuri ne domin bayar da furanni da lullubi a kanta, domin tabatarwa jama’a cewa musulmi masu son zaman lafiya da kaunar jama’a, sabanin yadda suke tunani.
Nakita Walrio shi ne mai kula da harkokin kasa da kasa a majalisar shawara ta musulmin kasar Canada, ya bayyana cewa hakika wannan abin da zata yan ada muhimmanci matuka, domin ko ba komai zai kara fito da dabiu na musulmi na son zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasar.
Musulmin kasar Canada dai suna nuna rashin gamsuwa da yadda masu kyamar muslunci suke ta karuwa a kasar, musamman a baya-bayan nan sakamakon karuwar ayyukan ta’addanci da wasu suke aikatawa da sunan addini a kasashen larabawan gabas ta tsakiya da ma wasu kasashen na turai.