IQNA

Masu Nakasa Uku Da Suka Hardace Kur’ani Mai Tsarki A Turkiya

22:37 - December 09, 2016
Lambar Labari: 3481018
Bangaren kasa da kasa, wasu masu nakasa su uku daga yankin Salwan da ke cikin gundumar Diyar Bakar na kasar Turkiya da suka samu hardace kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labarai na Anatoli cewa, Yusuf Gazaj tare da ‘yar uwarsa da kuma wani dan uwansa masu suna Kamerun da kuma Rashad, wadanda dukkaninsu suna da matsalar rashin gani, sun samu nasarar hardace kur’ani mai tsarki.

Rashad ta bayyana cewa ta samu nasarar hardace dukkanin kur’ani mai ta hanyar yawan maimatawa da kuma dagewa kan brinta na ganin ta samu hardace kur’ani mai tsarki, wanda kuma daga karshe Allah ya bata samun nasarar kaiwa ga wannan buri nata.

Ta ce hakika babban sirrin samun nasara a cikin kowane irin aiki shi ne tun farko mutum ya kasance yana da manufa ta yin hakan, sannan kuma ya zama yana son abun, sa’annan kuma ya bayar da himma ba tare da gajiyawa ba.

Kamerun ya ce shi ma da farko ya fuskanci matsaloli kafin ya kai samun wannan babbar nasara da Allah da Allah ya ba shi, domin kasantuwar cewa shi makaho ne, yana bukatar abubuwa da dama kafin ya iya kaiwa ga samun wannan nasara, to amma a cikin ikon Allah da taimakonsa, ya rika halarta ajin koyar da hardar kur’ani, wanda ta wannan hanyar ne ya iya samun damar hardace kur’ani mai tsarki.

Ya ce ya yi kokarin ganin ya kammala hardarsa acikin shekara guda daga lokacin da ya fara, to amma ba ta yiwu ba, amma cikin hukuncin Alah kafin ya cika shekaru biyu da fara hardar, ya samu damar hardace dukkanin kur’ani mai tsarki da taimakon Allah.

3552177


captcha