Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa
ya nakalto daga Shafin yada labarai na MIC ya habarta cewa, cibiyar PIO ta
kasar Amurka ce ta gudanar da wannan jin ra'ayin jama'a, wanda sakamakonsa ya
nuna cewa kimanin kashi 49 na Amurkawa suna kallon addinin muslunci a matsayin
addini tashin hankali.
Haka nan kuma kimanin kashi 82 cikin sun yarda da cewa lallai ana takura ma mabiya addinin muslunci a kasar tare da nuna musu kyama, duk kuwa da hakan ya saba wa dokokin kasar na 'yancin addini ga kowane dan kasa da bin irin akidar da ya natsu da ita.
A cikin rahoton baya-bayan nan da hukumar jami'an tsaro ta FBI ta bayar, ya nuna cewa ayyukan cin zarafi a kan musulmi a kasar sun karu matuka daga shekarar da ta gabata ta 2015 zuwa yanzu, inda aka kai hari kan musulmi sau 257, idan aka kwatanta da 2014, inda aka kai hari kan musulmi sau 154 a fadin kasar.
Kyamar musulmi da kuma baki yan kasashen waje ya karu ne akasar Amurka tun bayan da Trump ya fara yin kalaman batunci kan msuulmi da kuma baki mazauna kasar Amurka.