Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Amsato Sao Deby minister mai kula da harkokin mata da kuma kare hakkokin bil adama da kanan yara, ta bayyana agaban taron makon hadin kai a yau cewa, hakika mata suna da muhimmanci a cikin al’umma a cikin dukkanin bangarorin rayuwar da suka shafi al’umma.
Ta ce kasar Iran za ta iya zama a bin buga misali kan haka, inda ake damawa da mata a cikin dukkanin lamurra na zamantakewa da kuma, da hakan ya hada da iri rawar da suke takawa wajen tarbiyantar da al’umma a kan sahihin tafarki na rayuwa, wanda hakan ne kuma ya bayar damar gina al’umma ta gari mai kyakkayawan tunai da son zaman lafiya.
Ministar ta ce babban abin bakin ciki a halin yanzu kan al’ummar musulmi a tarwatse yake, kuma muna ganin cewa kasar Iran tana kiran taron hadin kai tsawon shekaru talatin, wanda hakan ke nuni da cewa hakika ta damu matsalar rarraban kan musulmi.
Babba abin da matsalar rashin hadin kan musulmi ta jawo musu a halin yanzu shi ne rashin kalama guda a cikin lamarinsu, wanda hakan shi ne kuma ya haifar da matsaloli, inda kowa ke yin abin da ya ga dama, har ma wasu daga cikin musulmin suna kafa kungiyoyin ‘yan ta’adda suna daukar nauyinsu da sunan addini, domin kuwa sauran musulmi kansu ba hade yake balanta a iya Dakar matakin ladabtar da duk wanda ya hakan.
Ta ce a matsayinta na minsiatr mata, tana bayar da shawar kan a karfafa kungiyoyin mata musulmi wajen fadakarwa da kuma wayar da kan matasa kan muhimamncin mayar da hankali ga koyarwar musulunci ta hakika maimakon bin duk wani abin ya zo na sabon yayi.