IQNA

An Kirayi Yahuwan Sahyuniya Da Su Mamaye Masallacin Aqsa

23:38 - December 26, 2016
Lambar Labari: 3481072
Bangaren kasa da kasa, kungiyoyin yahudawan sahyuniya sun kirayi sauran yahudawa da su mamaye masallacin aqsa maialfarma a lokacin idin yahudawa na Hanuka.

Kamfanin dilal;ncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewaya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Palastinu ya habarta cewa, kungiyoyin yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ati sun yi kira ga sauran yahudawan Isra’ila da su ammaye masallacin aqsa a karshen wanna mko domin gudanar da taronsu na Hanuka a a cikin masallacin.

Wannan taro dai za a gudanar ad shi a karkashin jagorancin wasu ‘yan majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra’ila wato Knesset, da suka hada da Yahuda Glik wanda malamin yahudawa ne mai tsatsauran ra’ayi, sai kuma wasu da suka hada da Migi Zuhar, Sholi Mualim, Professor Arye Aldad, Isra’il Aryel, Shimon Albium, wadanda dukkaninsu yahudawa masu tsatsauran ra’ayi.

Wasu daga cikin wadanda za su halarci wannan taro sun hada da fitattun ‘yan siyasa da kuma manyan jami’an gwamnatin Isra’ila, inda suke da nufin shiga cikin masallacin mai alfarma tare da keta alfarmarsa, ta hanyar yin shaye-shaye da shagulgula.

Yanzu haka dai yahudawan sun fara yin shirinsu na halartar wannan taro a cikin masallacin aqsa mai alfarma, kamar yadda kuma rundunar ‘yan sanda ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta fara shirinta domin ba su cikakkiyar kariya a lokacin shagulgulan da za su yia cikin masallacin mai alfarma.

3556738

http://iqna.ir/fa/news/3556738

captcha