Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na veto cewa, Muhammad Bentan ministan ma’aikatar kula da ayyukan hajji a Saudiyya, ya ce suna fatan ganin an warware takaddamar da ake yi kan batun halartar alhazai wurin aikin hajji daga Iran.
Ya ce ya aike da takardar gayyata ga ma’aikatar kula da ayyukan hajji da Umra da ziyara ta kasar Iran, domin neman a zauna a tattauna batun yadda za a bullo wa batun halartar alhazan kasar aikin hajji a shekara mai zuwa.
Babu wata majiya daga Iran da ta tabbatar da wannan ikirari, amma tuni jami’an kasar ta Iran suka bayyana cewa babbar matsalar da ta hana alhazan kasar zuwa aikin hajji ita ce, sun bukaci gwamnatin Saudiyya ta ba lamuni kan cewa za ta kare rayukan alhazan, domin ganin irin abin da ya faru na sakaci a Mina da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban alhazai da suka hada da daruruwan alhazan Iran bai sake faruwa ba, yayin da Saudiyya ta ce ba za ta ba Iran tabbacin cewa hakan ba za ta sake faruwa ba.