IQNA

23:21 - January 26, 2017
Lambar Labari: 3481173
Bangaren kasa da kasa, wasu ‘yan banga da ake sa ran jami’an tsaron masarautar Bahrain ne sun kai farmaki da bindigogi a kan masu zaman dirshan a kofar gidan Ayatollah Isa Kasim.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam cewa, mutanen sun zo ne a cikin bakaken kaya na dakarun kundimbala sun rufe fusakunsu, suna dauke da manyan bindigogi, inda suka bude wuta a kan masu tsaron gidan Ayatollah Isa Kasim.

Rahoton ya ce mutane da dama sun samu munanan raunuka, kamar yadda kuma suka ayi awon gaba da wasu, daga bisani sakamakon turjiyar da masu tsaron wurin suka yia gaban wadannan ‘yan banga, ala tilas sun janye da motoci 20 da suka zo da su.

Jim kadan bayan kaddamar da wannan hari, an jiragen yaki masu safkar angulu suna ta shawagi a wurin, yayin da sauran al’ummar kasar Bahrain suke ci gaba da isa wurin domin tabbatar da cewa wadannan ‘yan ta’adda ba su iya samun damar isa ga babban malamin addini na kasar ba.

Wannan harin ta’addanci ya zo bayan kwanakin da kisan kan da masarautar kama karya ta Bahrain ta yine a kan wasu matasa uku saboda dalilai na siyasa da banbamcin mazhaba, wanda kasashe da suke da’awar kare hakkin bil adama suka gum da bakunansu a kan lamarin.

3567010


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: