IQNA

Wata Musulma A Spain:
19:54 - February 05, 2017
Lambar Labari: 3481202
Bangaren kasa da kasa, Bishri Ibrahimi wata musulma ce da ke zaune a yankin Catalonia a cikin kasar Spain wadda ta bayyana cewa ba za ta iya samun gidan haya cikin cikin sauki ba saboda musulma ce.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, shafin yada labarai na bwabtk.com ya habarta cewa, yankin Catalonia mai cin gishin kai a kasar Spain, na daga cikin yanknan kasar da ake fama da matsalar nuna wariya da kyamar baki.

Rahoton ya ce jami’an tsaron yankin sun ce sun korafi dangane da matsaloli na nuna kyama ga baki a yankin har sau 292 a cikin yan lokutan nan, kuma 232 daga cikin korafin an same shi ne abirnin Bercelona fadar mulkin wannan tanki.

Bishri Ibrahimi wadda musulma ce ‘yar asalin kasar Morocco da take zaune a kasar ta Spain ta bayyana cewa, kimanin shekaru uku kenan tana zaune a yankin Catalonia, amma tana fuskantar matsaloli masu tarin yawa, da hakan ya hada har da rashin bata gidan haya, saboda ita musulma ce.

Ta ce a lokacin da take neman gidan haya tana shan wahala matuka, domin kuwa tana sanye lullbi a kanta, wanda ke nuni da cewa ita musulma, saboda haka masu gidan da sun fahimci haka sai su ki amincewa.

Amma idan har an samu to sukan kafa sharudda, wanda kuma sau da yawa ana kwarar masu karbar gidajen, amma saboda rashin mafita, dole za su karba koda an rubanya musu kudin hayar.

Kasar Spain dai na daga cikin kasashen turai da suka kusa da nahiyar Afirka, wadda bakin haure kan isa cikin kasar daga yankuna na kasashen Afirka musamman ma kasashen larabawan arewacin nahiyar, wanda yankin Catalonia na daga cikin yankunan da msuulmi suka fi zama.

3570744

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: