IQNA

19:57 - February 05, 2017
Lambar Labari: 3481203
Bangaren kasa da kasa, ana ci ci gaba da gudanar da jerin gwano a biranan Amurka domin la’antar Trump daga cikin jahohin har da Carolina ta kudu da Colarado.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na wyff4 cewa, al'ummar Amurka suna ci gaba da gudanar da zanga- zangar nuna adawa da bakar siyasar sabuwar gwamnatin kasar ta kokarin haifar da kiyayya kan al'ummar musulmi.

Jama’a a Amurka sun gudanar da zanga-zangar ce a birane da dama na kasar a yammacin jiya Asabar, inda suka cika manyan hanyoyin jihohin Denver, da Green well da sauransu , inda suke rera taken yin Allah wadai da bakar siyasar shugaban Amurka Donald Trump ta kokarin katange al'ummar musulmi daga shiga cikin kasar ta Amurka.

Har ila yau masu zanga-zangar sun yi ta rera taken neman ganin gwamnatin Amurka ta janyeaniyarta ta nuna kyamar bakin haure da 'yan gudun hijira daga kowace al'ummar duniya suka fito.

Tun a ranar Juma'a ashirin da bakwai ga watan Janairu da ya gabata ne shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan dokar takaita shigar baki 'yan kasashen waje da 'yan gudun hijira da suka fito daga wasu kasashen musulmi cikin kasar ta Amurka.

3570676


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: