IQNA

22:49 - February 06, 2017
Lambar Labari: 3481205
Bangaren kasa da kasa, kwamitin masallacin yankin Finsbury Park da ke birnin London ya gayyaci mabiya addinai daban-daban domin ziyartar wannan masallaci.

BKamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa ya nakalto daga jaridar Guardian cewa, fitaccen dan siyasa akasar Birtaniya Jeremy Corbyn kuma shugaban jam'iyyar Labour yana daga cikin wadanda suka karba wannan gayyata kuma suka ziyarci masallacin.

Mabiya addinin muslunci sun gudanar salla kamar yadda suka sab a cikin masallacin, yayin da sauran mutanen da aka gayyata suka tsaya suna kallonsu.

Bayan kammala salla musulmin tare da dukkanin wadanda aka gayyata sun zauna tare sun sha shayi sun tattauna batutuwa daban-daban, daga ciki kuwa har da irin yadda kyamar msuulmi ke karuwa a kasashen turai sakamakon kalaman batunci da Trump ke yi a kansu.

A lokacin da yake jawabi a masallacin, Corbyn ya bayyana cewa; dukkanin wadanda suka taru a wannan wuri ba musulmi ne kawai ba, a akwai mabiya addinai daban-daban, suna a matsayin bakin musulmi a wannan masallaci.

Ya ce wasu suna kallon muslunci da mummunan kallo alhali ba haka lamarin yake ba, domin basu mu'amala da msuulmi ne shi yasa suke kyamar msuulmi da kuma ayyukan ta'addanci da wasu ke aikatawa saia jingina hakan ga dukkanin musulmi, wanda kuma haka ba adalci ba ne.

Daga karshe an bayar da kyautukan kwafin kur'ani mai tsarki da kuma furanni ga dukkanin mabiya addinai da suka halarci masalalci.

3571087

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: