IQNA

23:45 - February 10, 2017
Lambar Labari: 3481218
Bangaren kasa da kasa, A yau ne al'ummar kasar Iran ke gudanar da bukukuwan cika shekaru 38 da samun nasarar juyin juya halin mulsunci a karkashin jagorancin marigayi Imam Khomenei, wanda ya yi sanadiyyar kawo karshen mulkin fir'aunanci da kama karya a kasar a karkashin masarautar kasar.

Bangaren kasa da kasa, A yau ne al'ummar kasar Iran ke gudanar da bukukuwan cika shekaru 38 da samun nasarar juyin juya halin mulsunci a karkashin jagorancin marigayi Imam Khomenei, wanda ya yi sanadiyyar kawo karshen mulkin fir'aunanci da kama karya a kasar a karkashin masarautar sarki Shah a cikin shekara ta 1979.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, Bayan samun nasarar kifar da gwamnatin Shah, Imam Khomeni ya bayar da dama ga al'ummar kasar da su zabi irin tsarin da suke so ya jagoranci, inda fiye da kashi 98 cikin dari na al'ummar kasar suka zabi tsari irin na addinin muslunci bisa zabinsu ba tare da wani tilasci ba.

Kafin samun nasarar juyin musulunci a Iran, kasar ta kasance babbar aminiya ga Amurka da Isra'ila a yankin gabas ta tsakiya, domin kuwa a lokacin Iran ta kasance ita ce mai aiwatarwa tare da kare manufofin Amurka da turawan yamma a yankin gabas tsakiya, wanda kuma hakan ya kawo karshe sakamkon samun nasarar juyin da aka yi a kasar, wanda kuma hakan ya ba kasar 'yanci na siyasa da tattalin arziki da zamantakewa da sauransu, kuma hakan shi ne babbar matsalar kasashen turai dangane da Iran, domin kuwa kafin juyin Islama su ne suke bata umarni, amma bayan juyi ba su isa su iya bata umarni ba, a kan haka suka daura damarar yaki da ita a dukkanin bangarori na siyasa da tattalin arziki da sauransu, tare da kallafa mata yaki har na tsawon shekaru 8 ta hanyar yin amfani da tsohon shugaban Iraki Saddam Hussain, da kuma kakaba takunkumai, amma duk da haka Iran ba ta taba mika wuya ba.

Sakamakon irin wadannan matakai na mayar da Iran saniyar ware da takunkumai, hakan yaba ta damar dogara da kanta da kuma bunkasa harkokin ilimi a dukkanin fagage, sakamakon hakan a cikin shekaru 38 da suka gabata ya zuwa yanzu, Iran ta zama daya daga cikin kasashen duniya 'yan kalilan da suke da fasahar sarrafa nukiliya a duniya, ta zama daya daga cikin kasashe masu ilimin kere-kere da karfin masana'antu, wanda hakan ne ma ya sanya faduwar farashin man fetur bai girgiza tattalin arzikinsu ba kamar yadda ya girgiza tattalin arzikin kasashen da suka doga da danyen man fetur da iskar gas.

Sakamakon tsayin dakan da Iran ta yi ne ya sanya ala tilas turawan da kansu suka bukaci zama kan teburin tattaunawa da ita domin warware takaddamar da suka jawo kan shirinta na nukiliya, inda daga karshe aka cimma matsaya kan shirinta wanda kuma har yanzu yake ci gaba da gudana daidai da yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakaninta manyan kasashe da kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, tare da amincewa da sharuddan da ta gindaya.

A sauran bangarori na ci gaban ilimin kimiyya da fusaha kuwa, a karkashin juyin juya halin muslunci a cikin shekaru 38 Iran ta kai matsayin da take harba tauraron dan adam da kanta zuwa sararin samaniyya, domin gudanar da ayyuka na bincike a sararin samaniya da kuma harkokin da suka da dangantaka da tsaro, kamar yadda kuma a mafi yawan fagage na aikin likita da hada magunguna ta dogara da kanta ne, haka lamarin yake a bangaren noma da samar da wadataccen abinci ga al'ummar kasa.

A bangaren karfin soji kuwa, Iran a halin yanzu tana daga cikin kasashen duniya da suke kera manyan makamai masu linzami da ke cin dogon zango, kamar yadda mafi yawan makaman da rundunar sojin kasar take da su manasa na kasar Iran ne suka kera su a cikin gida, ta yadda yanzu kasar ta zama ita ce mafi karfi ta fuskar soji a dukkanin yankin tekun fasha, haka nan kuma ta zama daga cikin kasashe mafi karfin soji a yankin nahiyar Asia, duk hakan ya kasance ne a cikin shekaru 38 bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci.

Ko shakka babu juyin juya halin muslunci da marigayi Imam Khomenei ya jagoranta ya dora tubulin ginin 'yantacciyar al'umma a kasar Iran bisa tunani na addini, wanda ya yi daidai da abin da muslunci ya koyar wajen yin tsayin daka domin bin gaskiya komai wahala, da kuma bijire wa karya da zalunci, domin tabbatar da adalci a cikin rayuwar al'umma a siyasance da kuma ta fuskar zamantakewa.

Wannan shi ne babban abin da yasa manufofin marigayi Imam Khomenei suka samu karbuwa a tsakanin dukkanin bangarori na al'ummar Iran, da hakan ya hada da malaman addinin muslunci, da kuma 'yan boko, gami da sauran masana a bangaroi daban-daban, da kuma sauran jama'ar kasa, wadanda suka hada da talakawa da 'yan kasuwa da kananan ma'aikata da sauransu, domin kuwa manufofin Imam Khomeni na kalubalantar sarki Shah da kuma tsarin sarauta da ke iko da Iran a lokacin, sun yi daidai da abin da kowane bangare na al'ummar kasar ke bukata.

Hakika al'ummomi da dama sun dauki darussa daga gwagwarmayar Imam Khomeni ta fuskoki daban-daban, musamman ganin cewa shi malamin addini ne, amma kuma juyin juya halin da ya jagoranta ya yi daidai da zamani da kuma siyasa da take tafiya tare da zamani, wanda hakan ne babban sirrin da ya sanya hatta wasu wadanda suke bin akidu na daban a kasar Iran da suka hada da 'yan gurguzu da kuma wadanda ba musulmi ba ne, su ma suka mara masa baya a lokacin juyin juya halin muslunci, domin kuwa sun san cewa manufar Imam Khomenei tafi dacewa da tsarin siyasa da zamantakewa ta dan adam.

Tasirin wannan yunkuri ya wuce kasar Iran, inda ya tsallaka har zuwa wasu kasashen duniya, duk kuwa da cewa tasirin hakan zai iya zama ta fuskoki da dama, da hakan ya hada da ci gaban ilimi, da kuma gwagwarmaya da fahimtar addini fahimta ta hakika, sabanin yadda wasu suke kokarin bayyana addini muslunci a matsayin addini na koma baya, da rashin wayewa ta zamani, hakika irin ci gaba da Iran ta samu a karkashin juyin mulsunci ya kawo karshen wannan mumman zato da wasu suke yi ma addinin musulunci.

3572788


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: