IQNA

23:50 - February 10, 2017
Lambar Labari: 3481219
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin wajen kaar Salvania ya aike da sakon taya murna ga jamhuriyar muslunci ta Iran kan zagayowar ranakun samun nasarar juyin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, Carl Victor Iryavich ministan harkokin Salvania kuma mataimakin firayi ministan kasar, ya aike da sakon taya murna ga ministan harkokin wajen Iran Muhammad jawad zarif, dangane da cika shekaru talatin da takwas da samun nasarar juyin juya halin muslunci.

A cikin sakon nasa yay aba da irin gagarumin ci gaban da aka samu ta fuskar alaka a tsakanin kasashen biyu, musamman bayan cimma yarjejeniyar nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.

Ya ce ana samun habbakar kasuwanci da cinikkaya da sauran harkokin tattalin arziki a tsakanin Iran da kasarsa, kuma wannan alaka za ta ci gaba da kara bunkasa a nan gaba domin amfanin kasashen biyu da al'ummominsu.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, yanzu haka kasashen biyu suna cikin tattaunawa ne kan bude ofisoshin jakadanci a tsakaninsu, ta yadda huldarsu za ta kara karfafa a dukkanin bangarori.

3572798


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: