IQNA

21:46 - February 14, 2017
Lambar Labari: 3481231
Bangaren kasa da kasa, Wani dan majalisar dokokin Amurka ya yi kakkausar suka a kan salon siyasar shugaban kasar Donald Trump ta kin musulmi da kuma baki a cikin kasar ta Amurka.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, Shafin yada labarai chicagotribune ya habarta cewa, an gudanar da wani taro a babbar cibiyar musulmi da ke birnin Naperville da ke jahar Illinois da ke kasar Amurka, inda dan majalisar dokokin kasar ta Amurka Bill Foster daga jam'iyyar Democrat ya samu halarta, bayan da musulmi suka aika masa goron gayyata.

Bill Foster ya gabatar da jawabia wurin taron wanda ya samu halartar Amurkawa musulmi da wadanda ba musulmi da kuma wasu 'yan kasashen ketare da suke zaune a Amurka, inda ya bayyana salon siyasar Donald da cewa ita ce siyasa mafi muni da Amurka ta taba gani a tarihinta, inda gwamnati take nuna wariya a tsakanin 'yan kasarta da suke da mabnbantan addinai da al'adu.

Ya ce abin da Trump yake ya sabawa dukkanin ka'idoji da dokokin ad suke cikin kundin tsarin mulkin kasar Amurka, kuma ci gaba da aiwatar da irin wannan salo na bakar siyasar Trump, zai zubar da kimar Amurka a idon duniya, lamarin da ya ce al'ummar Amurka ba za su zuba ido suna kallon haka na faruwa ba.

3574382
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: