IQNA

23:14 - February 15, 2017
Lambar Labari: 3481233
Bangaren kasa da kasa, bankunan gwamnatin kasar Aljeriya na shirin fara yin aiki da wasu tsare-tsare na bankin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya bayar da rahoton cewa, shafin ar.haberler ya bayar da rahoton cewa, Buallam Jabbar babban jami’I mai kula da harkokin saka hannayen jari a bankunan kasar Aljeriya ya bayyana cewa, bankunan gwamnatin kasar suna da shirin fara yin aiki da wasu tsare-tsare na musulunci a cikin harkokinsu.

Ya ci gaba da cewa yanzu haka dukkanin bankunan gwamnatin kasar guda bakwai sun shiga cikin tsarin, wanda za a fara yin amfani da shi nan ba da jimawa ba.

Kasar Aljeriya dai na bankuna guda 29 bakawai daga ciki ne kawai na gwamnatin kasar, amma sauran fiye da 20 mallakin kasashen yankin tekun fasha ne.

Dukkanin wadannan bakuna na kasashen yankin tekun fasha suna yin amfani da tsarin hada-hadar kudade bisa tsarin bankin muslunci, ta yadda mai kudi yake a matsayin daya daga cikin masu hannun jarin banki, kuma ana raba riba ne daidai abin banki ya samu na kudaden shiga, sabanin ribar da sauran bankuna suke bayarwa wadda aka kayyade.

Wannan mataki ya sanya da dama daga cikin mutanen kasar suka janye daga banknan gwamnati, suka koma ajiyar kudadensu a bankunan kasashen waje, kamar yadda kuma sun fi samun saukin karbar bashi daga gare su.

3574742

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: