IQNA

Ana Shirin Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani A Kasar UAE

22:50 - February 16, 2017
Lambar Labari: 3481235
Bangaren kasa da kasa, an ashirin fara gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a kasar hadaddiyar daular larabawa.
Ana Shirin Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani A Kasar UAE

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Khalij Times cewa, ya zuwa yanzu haka kimanin dalibai 1500 ne suka yi jrijistar sunayensu domin shiga wannan gasa.

Wannan gasa dai ta shafi matasa ne zalla , kuma an fara gudanar da ita tuna cikin shekara ta 2011, inda matasa masu shawar karatun kur'ani suke shiga gasar wadda Darul Bar yake shirya gudanarwa.

Abdullah Ali bin Zayid shi ne bababn darakta na cibiyar ta Darul bar ya bayyana cewa, wannan shirin na da nufin kara jawo hankulan matasa zuwa ga lamarin kur'ani mai tsarki, kuma a cewarsa ya zuwa yanzu wannan shiri ya samu gagarumar nasara fiye da yadda aka yi zato.

Ya ce lokacin da aka fara aiwatar da shiri kimanin shekaru biyar zuwa shida da suka gabata, matasa kalilan ne suke shiga shirin, amma yanzu a cikin shekara ta 2017, fiye da matasa dubu daya da dari biyar ne suka yi rijistar sunayensu, kuma har yanzu ana ci gaba da yin rijistar.

3575112


captcha