IQNA

21:50 - February 20, 2017
Lambar Labari: 3481248
Bangaren kasa da kasa, dubban Amurkawa sun gudanar da wani jerin gwano mai take (a yau ni ma musulmi ne) a birnin New York na kasar, domin kalubalantar salon siyasar Donald Trump ta kyamar musulmi da addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na «cleaveland.com» cewa wanann jerin gwano ya samu halartar dubban Amurka mabiya addinai daban-daban, domin nuna goyon bayansu ga musulmi da ake nuna musu kyama a hukumancea kasar, tare da nuna rera taken rashin amincewa da wannan salon siyasa na Donald Trump.

Kungiyoyin addini 50 ne suka shirya wannan gangami da jerin gwano, wanda magajin garin birnin na New York Bill de Blasio ya samu halarta tare da wasu daga cikin 'yan siyasa masu adawa da siyasar Trump.

Baya ga birnin New York wasu dubban Amurkawan sun gudanar da wani jerin gwanona birnin Los Angeles, inda su ma suka nuna rashin goyon bayansu ga wani sabon shiri da Trump yake da shi na sake fitar da wata doka da za ta hana musulmi daga kasashen da ya kayyada da kuma 'yan gudun hijira shiga cikin kasar Amurka.

3576266


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: