Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga tashar alalam cewa, masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain ta kame fararen hula 17 da suka hada da kananan yara 6 a cikin makon da ya gabata, amma daya daga cikinsu ne kawai ta saka.
Hakla na kumarahoton ya kara da cewa masarautar ta yanke hukunci a kan wasu fararen hla 19 a cikin wannan mako bisa dalilai na siyasa, 8 daga cikinsu kuma ta janye musu izinin zama ‘yan kasar.
A cikin wannan makon an gudanar da jerin gwano a yankuna 129 a kasar, jami’an tsaron gidan sarautar kasar sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye da kuma duka da kulake domin tarwatsa masu zanga-zangar a wasu yankunan.