IQNA

An Gudanar Da Taro Kan Hikimar Hijabi A Jami’ar Amurka

23:22 - March 02, 2017
Lambar Labari: 3481277
Bangaren kaswa da kasa, an gudanar da zaman taron kara wa juna sani kan hikimar hijabin musluncia jami’ar Glasburg da ke jahar Illinois ta kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na «webcache» cewa, kimanin mutane 65 wadanda ba musulmi ba ne suka halarci zaman taron, wanda ya yi dubi kan hikimar da ke tattare da saka hijabin muslunci.

A wurin Nabila Dadar wata daliba musulma da ke karatu a wannan jami’a ta gabatar da bayani, inda ta bayyana matsayin mace da kuma yadda musulunci yake bata kima ta musaman da kuma kare mutuncinta a cikin al’umma.

Ta bayyana cewa saka hijabi ga mata musulmi na daga cikin bangaren addininsu, domin kuwa muslunci yana sanya wasu abubuwa su zama wajibi wani lokaci saboda wasu dalilai na zamantakewa wadanda za a iya hankalta, wasu lokuta kuma umarni na ubangiji wandea yake da alaka da wani lamari na boye, wanda ba bayyananne ga mutum ba.

Hijabi yana daga cikin lamurra wadanda suke baya ga kasantuwarsu umanin ne na ubangiji wanda akwai wani abu na gaibi tattare da hakan, a lokaci guda kuma akwai wasu dalilai na zahiri wadanda hankali ma zai yarda da hakan.

Daga cikin irin wadannan dalilai kuwa har da yanayin rayuwar zamantakewa a cikin al’umma, inda muslucni yake kare mace yake suturce ta yake kare mata mutuncinta, tare da daukaka matsayinta a cikin jama’a.

Mata wadanda suke saka hijabi ko lullubi da kuma wadanda ba su yi hakan su ne za su iya fayyace hakan, domin a duk lokacin da mace ta yi lullubi za ta ji cewa tafi kamala, kuma hatta mutane sun fi ganin girmanta da mutunta, amma mace da take sabanin hakan ta fi saurin fuskantar matsala hatta daga mutane marassa mutunci marassa kintsi a cikin al’umma.

3579996


captcha