Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga Anatoli AA cewa, Donald Trump ya sake sanya hannu kan wata sabuwar dokar hana kasashen msuulmi 6 shiga cikin Amurka, bayan da kotu taki amincewa da dokar farko.
Kith Mouris Alison dan majalisar dokokin Amurka daga jahar Minnesota ya ce ba zai taba amincewa da wannandokar domin kuwa ta saba wa dukkanin dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar Amurka.
Shi ma Andrie Carson daga jahar Indiana ya nu na rashin gamsuwarsa da hakan.
Mai baiwa Trump shawara kan harkokin tsaro ta ce an samu sauyi a cikin sabuwar dokar inda aka cire Iraki daga cikin kasashen da dokar ta shafa, saboda hadin kan data bayar wajen bada bayyanan da ake bukata, aman matakin na nan daram akan sauren kasahen shida.
Haka zalika kuma a cewar jami'ar sauren baki da suke zaune Amurka masu takardar visa da katinzama kasar zasu samu kariya daga sabuwar dokar, kuma suma 'yan gudun hijira Syria zasu samu sukuni a wannan sabuwar dokar.
Idan ana tune wacen dokar ta farko daTrump ya sanyawa hannu a ranar ashin da bakawai ga watan Janairuta tanadi hana baki da kuma musulman wasu kasashe bakwai sanyakafa Amurkar, kafin daga bisani wani alkalin kotun tarayya yayi wasti da ita.