IQNA

Shirin Kara Fadada Ilimin Sanin Muslucni A Jami'ar Habasha

23:46 - March 15, 2017
Lambar Labari: 3481314
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin amnyan jami'oin kasar Habasha ta kudiri aniyar kara fadda bincike kan sanin addinin muslunci.

BKamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, a wata ziyara da shugaban ofishin yada al'adu na kasar Iran da ke kasar Ethiopia ya kai a jami'ar Makanisos, ya gana da manyan jami'anta

Daga cikin wuraren da ya ziyarta har da bangaren koyar da ilimin addinai na duniya, inda ya ganada shugaban bangaren wanda ya tabbatar masa da cewa,a a shirye suke su kar fadada ayyukansu wajen bincike kan addinin muslunci.

Wannan bangare dai yana gudanar da bincike da nazari kan addinin muslunci da kuma al'adu da suka shafi sauran al'ummomi, inda muslunci ya zama daya daga cikin amnyan addinai da ake koyarwa a wurin.

Akwai dalibai da dama yan kasar ta Ethiopia da kuma wasu 'yan kasashen waje da suke zuwa wurin domin karin ilimi.

Daga cikin muhimman abubuwan da aka cimma matsaya a kansu tare da shugabannin jami'ar da kuma cibiyar yad addini ta Iran, har da bayar da guunmawa ta kayayyakin aiki daga bangaren Iran ga wannan jami'a.

Haka nan kuma za a gayyaci mahuuntan jami'ar domin zuwa wasu daga cikin wurare na kasar Iran domin ganewa idanunsu waus daga cikin abubuwa na traihin muslunci a kasar.

Baya ga haka kuma an karfafa mahukuntan makarantar da sukai ziyara a sauran kasashen msuulmi musamamn wadanda suke da tarihi na mulsunci domin ganewa idanunsu abubuwa na tarhin muslunci.

3584672
Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Habasha ، Ethiopia ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha