IQNA

Amurka Ta Kashe Mutane 42 A Wani Masallci A Syria

22:55 - March 17, 2017
Lambar Labari: 3481322
Bangaren kasa da kasa, jiragen yakin Amurka sun kaddamar da wasu hare-hare a kan wani masallaci da ke a wani kauye da cikin gundumar Aleppo, inda suka kashe mutane 42 tare da jikkata wasu fiye da dari daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, rahotanni daga kasar ta Syria sun tabbatar da cewa, jiragen na Amurka sun kaddamar da harin a lokacin da mutane suke sallar magariba a masallacin, wanda yake a wani kauye da ke karkashin ikon 'yan bindiga masu tayar da kayar baya.

Da farko dai Amurka ta musunta cewa jiragenta sun kai hari, amma daga bisani ta ce jiragen sun kai hari amma a kan wani wuri ne da 'yan alka'ida suka taru.

Harin an Amurka dai a kan masallatai da wuraren hada-hadar jama'a a cikin Syria ba shi ne na farko ba, kuma tana kai hare-haren ne da sunan yaki da 'yan ta'adda.

Amurka da wasu daga cikin kasashen turai musamamn Birtaniya da faransa, da kuma wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya da suka hada da Saudiyya, Qatar da kuma Turkiya, su ne kan gaba wajen daukar nauyin dukkanin kungiyoyin 'yan ta'adda da ke kai hare-hare a cikin kasar Syria, domin kifar da gwamnatin Bashar assad, wanda baya dasawa da kasashen yammacin turai.

3584877

captcha