IQNA

An Kafa Sakandami A Wurin Ginin Masallaci A Jamus

23:45 - March 18, 2017
Lambar Labari: 3481325
Bangaren kasa da kasa, wasu masu kyamar musulmi a kasar Jamus sun kafa sakandami a wani wuri da ake shirin gina masallaci a garin Erfurt na kasar Jamus.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Nidaul Watan cewa, a jiya wasu mutane masu tsnanin kiyayya da musulmi sun kafa sakandami domin nuna rashin amincewarsu da wani shirin ginin masallaci a garin Erfurt.

Kafin wannan lokacin dai jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya ta kasar ta aike da wani sako ga mahukuntan birnin Erfurt, da ke neman a hana ginin wani masallaci a birnin, amma mahukuntan sun yi watsi da wannan bukata.

Musulmi mazauna birnin ne suka bukacia ba su damar gina masallaci domin gudanar da harkokinsu na addini a wurin, amma an samu rabuwar kai a tsakanin mutanen wannan birni kan wannan batu.

Masu nuna adawa da shirin na fakewa da hujjar cewa, gina masallaci a wannan gari zi jawo karuwar ‘yan gudun hijira su rika zuwa wrin, a hankali kuma za su cika musu gari, yayin da masu goyon bayan lamarin ke ganain cewa, yin hakan ba laifi ba ne, domin kuwa bai saba ma ko daya daga cikin dokokin kasar ba.

Kamar yadda suka bayyana karbar bakia matsayin tabia mai kyau da ya kamata su nuna ma masu gudun hijira, domin kwa suma mutane ne kamar kowa.

3584972

captcha