Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, jami’an tsaron kasar Bahrain a cikin kayan sarki sun kaddamar da farmaki a kan gidajen jama’a a yankuna daban-daban a cikin birnin Manama da kewaye, inda suka kame mutane 23 da suka hada da kananan yara guda shida.
Baya ga haka kuma a cikin wanann makon kotun masarautar ya yanke hukuncin kisa a kan wasu ‘yan siyasa masu adawa su 3, yayin da kuma aka yanke hukuncin daurin rai da rai a kan wasu ‘yan siyasa su 8, bisa tuhumar cewa suna adawa da siyasar masarautar kasar, kamar yadda kuma aka janye izinin zama dan kasa a kan wasu ‘yan siyasa tara, da suka hada har da tsohon dan majalisar dokokin kasar Hassan Isa, wanda shi ma aka daure shi shekaru 10 a gidan kaso, saboda yana adawa da siyasar mahukuntan kasar
Rahoton ya ci gaba da cewa, masarautar Bahrain ta dauko hayar jami’an tsaro daga kasashen ketare domin murkushe duk wani al’ummar kasar da suke neman hakkokinsu a matsayinsu na ‘yan kasa, a lokaci guda kuma masarautar ta Bahrain tana samun cikakken goyon baya daga kasashen Amurka da Birtaniya musamman.