IQNA

Gasar Kur'ani Ta Dalibai Da Ke Karkashin Azhar

19:24 - April 04, 2017
Lambar Labari: 3481374
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta daliban makarantu da ke karkashin cibiyar Azhar a Masar.

Kamfanin dillancin labarankur'ani na iqna ya ahbarta cewa, an fara gudanar da gasar wadda ke gudana karakshin sa idon Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azhar da kuma Muhamamd abu Zai Almair, shugaban dukkanin cibiyoyin Azhar bangaren kur'ani.

Wannan gasa dai tana samu halartar daliban makarantun firamare da sakandare bangaren faro da kuma bangare na biyu, tare da halartar dalibai 82 daga dukkanin sassan kasar Masar a karkashin cibiyoyi 27.

Daga karshe za a fitar da dalibai 30 ne wadanda suka nuna kwazo wadanda kuma za su karbi kyautuka na musamman a bangaren hardar kur'ani mai tsarki.

Cibiyar Azahar ta jima tana shirya gasar hardar kur'ani ta kasa baki daya, da ke samun halartar dalibai a bangarori daban-daban, da nufin raya lamarin kur'ani mai tsarki a cikin zukatan matasan kasar ta Masar.

3586638

captcha