Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin kamfanin dillancin labaran Anatoly AA cewa, Firuz ‘yar shekaru 69 ta himmatu matuka wajen hardar kur’ani mai tsarki.
Wannan mataki da wannan mata ta dauka, ya biyon bayan rashin samun damar yin hakan ne a lokacin kuruciyarta, inda a halin yanzu ta fahimci cewa kur’ani mai tsarki na da muhimamnci fiye da yadda ake tsammani a rayuwar mutum musulmi.
Ta bayyana cewa, alokacin tana karama ta fara yin karatun kur’ani amma ba ta yi nisa ba sai aka yi mata aure, daga lokacin da ta fara haihuwa kuma sai hidimar kula da yara da shagaltar da ita.
Ta kara da cewa, wannan ya sanya ta zama tana tuhumar kanta kan mene yasa za ta daina bayar da lokacinta ga kur’ani gas hi har tsufa ya riske ta, a kan haka ta yanke shawara ta koma karatun kur’ani gadan-gadan, inda a halin yanzu kuma ta shiga harda, har ta kai rabin kur’ani, kuma tana ci gaba da domin ganin ta samu damar hardace kur’ani baki daya.
Dangane da lokacin da ta dauka a wajen hardar kuwa, ta bayyana cewa hakika ta samu taimakon Allah madaukakin sarki, domin kuwa daga lokacin da ta fara hardar zuwa lokacin da ta hardace rabin kur’ani, bai dauke ta lokaci mai tsawo ba.