IQNA

Palastinawa Sun Yi Sallar Juma’a A Wajen Masalalcin Aqsa

23:30 - April 09, 2017
Lambar Labari: 3481391
Bangaren kasa da kasa, sakamakon killace masallacin aqsa da yahudawan sahyuniya suka yi a wannan mako palastinawa sun yi salla a wajen masalalcin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun fara kaddamar da farmaki a kan musulmin Palastine a birnin Quds, tare da yin awon gaba da wasu matasa.

Sojojin na Isra'ila a cikin kayan sarki da motoci masu sulke, sun kutsa a cikin yankunan Palastinawa da ke a gabashin birnin Quds, inda suke karya kofofin gidajen jama'a suna kame matasa suna yin awon gaba da su.

Haramtacciyar kasar Isra'ila ba ta bayar da wani dalili na yin wannan kame ba, amma dai wasu Palastinawa na ganin hakan baya rasa nasaba da shirin gudanar da idin yahudawa da za a yi, inda palastinawa musamman ma matasa daga cikinsu kan hana yahudawa shiga cikin masallacin, domin kare alfarmarsa.

A daidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da cin zarafin palastinawa da keta alfarmar wurare masu tsarkia birnin quds, babu ko daya daga cikin kasashen larabawa da ta ce uffana akan wanann lamari.

3587650


captcha