Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a wani taron karawa juna sani da ya gudana a yau a birnin Nairobi na kasar Kenya, mataimakin limamanin Juma’a na Nairobi ya bayyana muhimmanci ci gaba da wayar da kan jama’a a masallatai.
Sheikh Juma’a Amir shi ne mataimakin babban limamain masallacin Juma’a na birnin Nairobi, ya bayyana wannan taron karawa juna sani wanda ya kunshi malamai da limamai na kasar Kenya cewa, masallaci ba wurin salla ne ba kawai.
Malamin y ace akwai abubuwa da dama na yada al’adun muslunci da ilmantarwa, da ma taruka na addini domin karawa juna sani wadanada duk za a iya gudanar da su a masallatai, wanda kuma hakan zai taimaka domin nan wurin da musulmi suke zuwa kullum har sau biyar a rana.
Daga karshe ya yi kiira ga limamai da su zama mas bayar da gudunmawa wajen fadakar da msuuli kan hakikanin abin da musulunci ya koyar, da kuma kaucewa duk wani abin da zai batawa musulunci suna a duniya.