IQNA

Wani Dalibi Daga Canada Ya Yi Karatu A Gefen Gasar Kur’ani

23:23 - April 23, 2017
Lambar Labari: 3481432
Bangaren kasa da kasa, wani dalibi dan kasar Canada da shekarunsa ba su wuce 12 ba ya gudanar da karatun kur’ani mai tsarki a gefen gasar da ake gudanarwa a kasar Iran.

Muhammad Manuf Hussain wanda shi ne wakilin kasar Canada a gasar kur’ani da ake gudanarwa a Iran, ya bayyana cewa ya samu nasara a karatun kur’ani ne tun yana da shekaru da ba wuce biyar a duniya ba.

Ya ce mahaifansa sun taka gagarumar rawa wajen hganin sun dora shia kan turba ta karatun kur’ani mai tsarki, kasantuwar mahaifinsa makaranci ne kuma mahardacin kur’ani mai tsarki, wanda ya taimaka masa matuka awannan bangare.

Haka nan kuma ya yi shara da yadda mahaifinsa ya dora shi a kan hanya mafi sauki wajen hardace kur’ani a lokacin da yake da shekaru biyar, wanda kuma da ikon Allah ya samu nasarori ta hanyar yin amfani da shawarwarin mahaifinsa.

Muhammad wanda dan asalin kasar Bangaledah ne, ya ja hankulan matasa musulmi saoinsa da su mayar da hanklai ga lamarin kur’ani mai tsarki, domin dukkanin rabo da dacewa na duniya da lahira na cikin sanin kur’ani da yin aiki da abin da yake koyar da mu.

3592494

Wani Dalibi Daga Canada Ya Yi Karatu A Gefen Gasar Kur’ani

captcha