IQNA

Karuwar Ayyukan kyamar Musulmi A Kasar Amurka

23:59 - April 26, 2017
Lambar Labari: 3481442
Bangaren kasa da kasa, an kara samun karuwar kyamar msuulmia cikin yankuna da daman a kasar amurka a cikin yan kwanakin nan.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga jaridar Independent cewa, an kara samun karuwar kyamar msuulmia cikin yankuna da daman a kasar amurka a cikin yan kwanakin da suka gaba ta a ya zuwa.

Daga cikin yankunan da aka samu wannan matsala kuwa har da manyan biranan kasar, inda musulmi suke fuskantar wulakanci da tozarci daga mutanen gari, yayin da kuma hukumomi bas u daukar matakan da suka dacea kan wannan lamari.

A cikin yan watannin da suka gaba, hare-haren da aka kai kan musulmi da masallatai da kuma cibiyoyi da wuraren ibada na msuulmi a gfadin Amurka ya lunka sau dubu aya idan aka kwatanta da lokutan baya.

Ynzu haka dai cibiyar musulmin Amurka ta ce tana daukar dukkanin matakan da suka dace domin fuskantar wannan lamari ta hanyoyin doka da kuma da shari'a domin kuwa wasu bas u san komai sai ta hanyar shari'a.

3593544

captcha