IQNA

An Sake Tado Da Batun Faduwar Kugiya A Masallacin Harami

20:20 - May 05, 2017
Lambar Labari: 3481485
Bangaren kasa da kasa, an sake tado batun faduwar kugiya a cikin masallacin haramin Makka mai alfarma wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar alhazai da dama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta alarabiyyah mallakin Saudiyya da ke watsa shirinta daga birnin Dubai ta bayar da rahoton cewa, wata kotun daukaka a kara a kasar Saudiyya ta sake dawo da batun shari'ar mutanen da suke hannu a kan batun faduwar kugiya a kan masallacin harami kusans hekaru biyu da suka gabata.

A lokutan baya kotun da ke gudanar da bincike kan batun ta wanke mutanen da ake zargi da yin sakaci, wanda sakamakon hakan ne wannan kugiyar ta fado a kan jama'a a cikin masallacin haramin Makka mai alfarma.

Kotun daukaka karar ta ce tana zargin mutane 13 ne sabanin mutane 14 da aka zarga baya, da suka hada da wani hamshakin mai kudi dan kasar ta Saudiyyah, sai kuma wasu 'yan kasashen Pakistan, Canada, Philipines, Jordan, Palastinu, masar da kuma hadaddiyar daular larabawa.

Hadarin wanda ya faru a lokacin da ake shirin fara aikin hajjin sekaru biyu da suka gabata, ya yi sanadiyyar mutuwar alhazai 111 da suka fito daga kasashen duniya daban-daban, yayin da wasu kimanin 240 suka samu raunuka, mahukuntan Saudiyya sun yi alkawalin biyar diyyar wadanda suka rasa rayukansu, amma kuma daga lokacin bas u kara tayar da zancen ba.

3596118


captcha