Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin khabarmasr cewa, babban masallacin Azahar ya sanar da cewa, wanann gasa za a gudanar da ita ne kamar yadda aka saba gudanarwa a kowace shekara, kuma za ta fara ne daga ranar Asabar mai zuwa tsawon kwanaki biyar.
Bisa ga a'alda dai ita wannan gasa ana gudanar da ita ne a tsakanin daliban jami'ar masu karatun kur'ani, inda akan zabi wadanda sautinsu yafi kyau domin su rika gudanar da karatu a gidajen radiy da kuma talabjin na kasar, da kuma lokutan bude wasu taruka ko kuma rufewa.
Gasar ta hakan hada da bangaren mata da kuma maza, a wannan karon gasar za ta hada 'yan kasar ta Masar da kuma 'yan kasashne ketare da suke karatu a wannan jami'a, inda za a fitar da wasu daga cikinsu wadanda sautinsu ya fi kyau a matsayin wadanda za su lashe gasar.
Wadanda suka samu nasarar lahe wanann gasa, za su kasance daga cikin wadanda za su gudanar da shirin karatun kur'ani na wata Ramadan na wanann shekara, wanda yake farwa daga ranar 19 ga watan na Ramadan, kamar yadda a ka kafa sharadin cewa makarantan dole ne shekarunsu ya zama kasa da talatin da biyar.