IQNA

Makaranci Dan Shekaru 13 Daga Canada Na Halartar Gasar Malaysia

19:53 - May 18, 2017
Lambar Labari: 3481525
Bangaren kasa da kasa, makarancin kur’ani na uku a rana ta uku a gasar kur’ani da ake gudanarwa a Malaysia ya haskaka gasar da karatunsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta daga birnin Kualalampoour cewa, makarancin kur’ani na a rana ta uku agasar Malaysia ya farantawa mahalarta gasar rai matuka.

Makarancin na daren jiya Muhammad Ma’aruf Hussain dan shekaru 13 daga kasar Canada ya gudanar da tilawa a cikin surat muminin, inda ya nuna kwarewa matuka da kuma yin salo mai jan hakali matuka, wannan matashi dai ya halarci gasar kur’ani ta Iran, da Qatar da kuma Malayisa, inda a iran a bangaren karatun a gasar kur’ani ta ‘yan makaranta ya zo a matsayi na biyu, a kasar Qatar kuwa ya zo a matsayin na daya.

Bayan ya kammala karatun nasa ya zanta da manema labarai, inda ya yi bayani kadan dangane da rayuwarsa.

Ya bayyana cewa tun kimanin shekaru 5 da suka gabata ne ya fara yin karatu a fagen kwararru, daga bisani kuma ya fara halartar gasar kur’ani ta duniya a kasashe daban-daban, amma cewarsa idan akwai makaranta daga Iran da Malaysia lamarin yana da wahala a gare shi ya iya lashe gasar.

3600681


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha