Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Alwatan News cewa, an samu wasu daga cikin shagunan sayar d alittafai a cikin kasar Masar suna sayar da kwafin kur'ani mai tsarki da lasisin bogi na Azhar ga jama'a.
Wadannan kur'anai da ake buga su da kaloli tun a cikin shekara ta 2015 da gabata ce cibiyar Azhar ta sanar da hana sayar da su a cikin kasar ta Masar baki daya, amma duk da haka 'yan kasuwa sun yi lasisi da yake a kan kwafin kur'ani, da ke nuna cewa Azhar ta amince a sayar da shi.
Kwafin kur'anin wanda ake kira da Abu Warda saboda kalolinsa, ana sayar da karamin kwafi a kan fan 40 na Masar, babban bugu kuma akan fan 70 a cikin dakin sayar da littafai da ke bayan masallacin Alhussain da ke cikin birnin Alkahira.
Abdulwahab daya ne daga cikin masu sayar da irin wannan kwafin kur'ani mai launuka ya bayyana cewa akwai izinin sayar da wannan kur'ani daga cibiyar Azahar, kuma mutane suna son sa matuka, musamman a yanzu da azumi ke karatowa, inda suke saye suna bayarwa kyauta.
Sai dai a nasa bangaren Muhammad Shuhhat daya daga cikin mambobin kwamitin cibiyar Azhar da ke sanya ido kan buga littafai a kasar ya bayyana cewa, wannan kur'ani bas hi da lasisi, kuma mutane suna sayar da shi da farashi mai tsada, musamman a halin yanzu da azumi ke karatowa.