IQNA

Kasashe 22 Ne Halartar Baje Kolin Kur'ani Na Kasa Da Kasa

23:44 - June 03, 2017
Lambar Labari: 3481576
Bangaren kasa da kasa, Abbas Nazaridar shugaban bangaren kasa a kasa na baje kolin kur'ani na duniya da ke gudana a Tehran y ace kasashe 22 ne ke halartar taron.
Abbas Nazaridar a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu wakilan madaba'antu daga kasashe 22 ne suke halartar baje kolin kur'ani na kasa da kasa da ke gudana a birnin Tehran.

Ya ci gaba da cewa wannan shekara an samu karuwar baki daga kasashen ketare da suka halarci wannan babban baje koli, kuma za a ci gaba da gudanar da shi har zuwa karshen watan Ramadan mai alfarma.

A wannan baje kolin dai an nuna wasu daga cikin kayayyakin da suka shafi kur'ani da ake bugawa a Iran, da suka hada kwafi-kwafi na kur'ani da kuma na'urori iri-iri da suke dauke da shirye-shirye daban-daban kur'ani, da suka hada da na'urori masu kwakwalwa da sauransu.

Wannan dai shi ne karo na 25 da ake gudanar da wannan babban taro na baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya a birnin Tehran, inda da dama suke amfana da wannan baje koli a kasar Iran wajen samun sabbin hanyoyi na koyon karatun kur'ani da harda na zamani.

Haka nan kuma suna karuwa da wasu abubuwa da suka shafi kur'ani wadanda ake zuwa da su daga wasu kasashen, kamar masar da sauransu, wadanda sun yi nisa a akn sha'anin kur'ani mai tsarki.

Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da wannan baje koli kamar yadda aka tsara, inda madaba'antu da dama da sue buga kur'ani da kuma masu ayyukan fasahar rubutun ayoyin kur'ani duk suke halartar wannan wuri na baje kolin kur'ani na duniya.

3605657


captcha