IQNA

Janye Dokar Kayyade saka Hijabi A Wata Makarant A Firka Ta Kudu

23:54 - June 09, 2017
Lambar Labari: 3481596
Bangaren kasa da kasa, an janye wata dokar kayyade saka hijabin muslunci a wata makaranta da ke birnin Johannesburg kasar Afirka ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai Dunya Bulletin cewa, kwamishinan ilimi na gundumar Gauteng a kasar Afirka ta kudu ya bayyana cewa, sun janye wata doka kan batun kayyade saka hijabi da wata makaranta ta kafa a kan dalibai mata.

Kwamishinan ya bayyana cewa, sun samu kurafi da dama daga iyayen yara kan yadda ake takura musu da kuma nuna musu bangaranci a kan banbancin addini, a kan haka suka dauki mataki fuskantar wannan lamari.

Ya ci gaba da cewa, iyayen yara sun sanar da su cewa, ana tilasta yayansu cire hijabin musluncia duk lokacin dasuka zo makaranta, ko kuma a tilasta su rike wani kati na musamman da ke nuna cewa an bas u izinin saka hijiabin a cikin makarantar.

Jami'in ya ce irin wadannan matakai sun hannun riga da dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar Afirka ta kudu, wanda ya bayar da izinin yin addini ga kowane mutuma cikin kasar, a kan haka ya ce sun janye wannan doka kuma ba za su taba amincewa da wani abu makamancin haka ba.

3607696


captcha