IQNA

An Gano Wasu Ababe Na Tarihi masu Alaka Da Musulmi A Ethiopia

23:53 - June 17, 2017
Lambar Labari: 3481619
Bangaren kasa da kasa, masana kan harkokin tarihi da abubuwan tarihi sun gano wani wuri da yake dauke da wasu abubuwa da ke nuna alakar wurin da musulmi a Ethiopia.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga archaeology masu gudanar da bincikn sun ce wurin yan adauke da wasu abubuwa na tarihi wadanda suke da alakada da kasashen musulmi kuma tarihinsu yana komawa zuwa ga shekaru fiye da dari bakawai.

Daga cikin abubuwan da aka samu akwai tsoffin karau da kuma wuri gami marmar da gilassai wadanda msuulmi suke amfani da su daga kasashen Madagaska da Maldiv Yemen da kuma China.

Timosy Insel daga kasar Birtaniya masani ne a kan gano abubuwan tarihi ya bayyana cewa, akwai wani wurin kasuwanci da kuma masallatai da wasu ciciyoyi da aka samu a wurin, sun kama da ginin masallatan Tazania da kuma Somalia.

Ya ce ganin wadannan abubuwa ya sanya sun kara samun tabbaci a kan cewa hakika wurin yana da alaka da musulmi, baya ga haka kuma sun samu kudade na zinari da azufa ga kuma tagwalla, wadanda aka yi musu zane da ke nuna alama ta musulunci.

Yanzu haka dai an dukufa wajen gudanar da bicnike a kan wadannan abubuwa domin kara samun tabbacia kansu da kuma tarhinsu.

3610437


captcha