Daga cikin abubuwan da ya ambata kuwa har da gudanar da ayyukan maniyyata a birnin Jidda da kuma daukarsu cikin sauki ba tare da bata lokaci ba zuwa birnin Madina, inda a can ma za a gudanar da wasu shirye-shirye na musamman domin tabbatar dacewa ba a su fuskanci wata matsala ba.
Baya ga haka kuma a lokacin gudanar da aikin hajji a Makka za a kula da su yadda ya kamata, tare da kama musu wurare masu nagarta da kuma ba su wadatattun kudaden guzuri.
Kasar Ghana dai tana daga cikin kasashen Afirka wadanda suke da musulmi da suke halartar aikin hajji a kowace shekara, duk kuwa da cewa aikin hajjin bana yana da tsare-tsare sakamakon Karin kudade daga mahukuntan Saudiyya, amma duk da haka ba mahukuntan na Ghana sun sha alwashin kyautata ma alhazansu.