IQNA

Ministan addini na Masar:

Ba A Biyan Kudi Wajen Koyon Karatun Kur'ani

17:44 - July 03, 2017
Lambar Labari: 3481667
Bangaren kasa da kasa, ministar mai kula da harkokin addini a kasar Masar ya bayyana cewa ba zasu taba bari a karbi kuadde domin koyar da kur'ani ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na massai.ahram cewa, Muhammad Mukhtar Juma'a ministar mai kula da harkokin addini a kasar Masar ya bayayan cewa, ko alama ba zasu taba bari a karbi kuadde domin koyar da karatun kur'ani ko hardarsa ba.

Ya ci gaba da cewa koyar da karatun kur'ani a kasar Masar baki daya kyauta ne babu inda aka amince da karbar kudade, domin kuwa ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar ce take da alhakin biyan kudade ga malamai da suke da kur'ani ba iyayen yara ba.

Daga karshe ya bayyana cewa za su ci gaba da yin aiki tare da malaman kur'ani da makarantun islamiyya domin hana yada tsatsauran ra'ayi da sunan addini a makarantun kur'ani da kuma wasu cibiyoyi da aka bude da sunan addini da suke koyar da akidun da ke sa matasa shiga kungiyoyin 'yan ta'adda.

Kasar Masar dai tana daga cikin kasashen msuulmi da suke bayar da muhimmanci matuka ta fuskar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a tsakanin kasashen musulmi.

3614952


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha