IQNA

UNESCO Ta Saka Birnin Alkhalil Da Masallacin Annabi Ibrahim A Cikin Wuraren Tarihi

23:47 - July 07, 2017
Lambar Labari: 3481679
Bangaren kasa da kasa, hukumar kula da adana wurare da kayayyakin tarihi ta duniya UNESCO ta saka birnin Alkhalil da kuma masallacin annabi Ibrahim a cikin wuraren tarihi na duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na al-ahad cewa, hukumar UNESCO ta bayyana wadannan muhimamn wurare na Palastinawa a matsayin manyan wuraren tarihi na duniya.

Rula Ma'ayi'a ministan kula da harkokin yawon bude ido a Palastinu ta bayyana cewa, hakika wannan banban ci gaba ne ga al'ummar Palastinu, musaman ma yadda hukumar UNESCO ta tabbatar da wannan wuri a matsayin daya daga cikin wuraren tarihi na Palastinawa.

Sai dai bangaren ministan yakin harammtacciyar kasar Isra'ila Avigdor Lieberman ya bayyana hakana matsayin wani abin bakin ciki, domin kuwa a cewarsa UNESCO ta kara tabbatar da halascin Palastinawa, tare da bayyana cewa hukumar UNESCO na daga cikin hukumomi masu adawa da Isra'ila.

3616208


captcha