Wannan dai yana daga cikin muhimamn lamurra nab akin ciki da suka wakana a wannan yanki inda Sabiuawa suka yi musulmin kisan kiyashi a kan idanun al'ummomin duniya ba tare da wani taimako ba.
An gudanar da taron na bana ne tare da wani karin bakin cikin bayan gano wasu kabruka na mutane 71 da aka kasha tun a lokacin da ba a san da zamasnsu ba.
Haka nan kuma taron na bana ya samu halartar jakadun kasashen duniya musamman na musulmi da suka hada da na jamhuriyar muslunci ta Iran gami da iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, kamar yadda kuma malaman addini na kasar gami da jami'an gwamnati da kuam kugiyoyin farar hula duk sun halarci wurin.
Kasar Bosnia na daga cikin kasashen nahiyar turai da aka sarin mazauan kasar musulmi ne, wanda hakan ne ya kara bayar da dama ga masu tsananin kiyayya da muslunci daga cikin sabiyawa a lokacin suka yi kisan gilla a kan msuulmi na wannan kasa.