Ya ci gaba da cewa babban lamarin da ke da muhiamnci shi ne, gudanar da shiri mai amfani ga jama'a masu saurare, domin kuwa wannan gidan radiyo shi ne irinsa na farko da aka taba bude a tarihin kasashen msuumi, wanda kuma yake ci gaba da gudanar da shirinsa sa'oi ashirin da hudu ba tare da tsayawa ba.
Kwamitin kula da harkokin karatu na wannan gidan radiyo ya sanar da cewa,a wanann shekara an dauki wasu sabbin matasa makaranta wadanda ba a san da su, wadanda za su kasance taurarin karatu a wannan tasha, baya ga tsoffin da aka saba da su.
Hasan Sulaiman shi ne babban daraktan wanann tashar radiyo, ya kuma bayyana cewa ana samun gagarumin ci gaba adukkanin bangarori na shirye-shiryen gidan radiyon.
Abul Ala Habin shi ma wani fitacen makarancin kur'ani ne dan kasar masar wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa ga wannan gidan radiyo, inda shi ma ya yaba da ci gababn da ake samu.