Bahram Qasemi ya ce wannan rahoto bai zo wa Iran da mamaki ba, domin kuwa babbar manufar Amurka ita ce bayyana kiyayyarta ga Iran, da kuma kokarin ganin ta wawantar da sauran al'ummomin duniya, alhali kuwa tuni kan mage ya waye.
Qasemi ya ce dukkanin al'ummomin duniya da su kansu al'ummar Amurka sun san kasashen da suka kirkiro 'yan ta'adda kuma suke mara musu baya, domin kuwa al'ummar Amurka sun san wadanda suka kai musu hari a ranar 11 ga watan Satumban 2001 a biranan New York da Washington, domin akidar 'yan ta'adda a bayyane take ga kowa a duniya, kasashen da suke dauke da irin wannan akida su ne manyan kawayen Amurka a yankin gabas ta tsakiya, kuma su ne suke yada akidar ta'addanci da sunan addini tare da taimakon Amurka, saboda dalilai na siyasa da tattalin arziki, wanda hakan bayyane yake ga kowa kamar hasken rana.
Ya kara da cewa, rahoton na Amurka ya zargi Iran da cewa ita ce kasar da take mara baya ga ta'addanci da 'yan ta'adda a duniya, amma bai ambaci kungiyoyin 'yan ta'addan ba, sai kungiyar Hizbullah saboda tana kare kasar Lebanon daga hankoron mamayar Isra'ila, da kuma taimaka ma gwamnatin Syria da take yi wajen yaki da kungiyoyi irin su ISIS da makamantansu, amma rahoton yaki ya ambaci kungiyoyin da su ne 'yan ta'adda bisa dokokin duniya, irin su ISIS alqa'ida da makamantansu, kan su wane ne suke daukar nauyinsu, ba domin komai ba, sai saboda hakan ya saba wa maslahar siyasar Trump ta jari hujja, domin kuwa da kudin da aka kafa irin wadannan 'yan ta'adda kuma ake daukar nauyinsu ne ake sayen makamai daga Amurka har na daruruwan biliyoyin daloli.
A kan hakan Qasemi ya ce zargin Iran da taimaka 'yan ta'adda masu kai hare-harea duniya ya kara zubar da mutuncin Amurka ne da sa al'ummomin duniya yin shakku kan a duk abin da take fada a kan wasu batutuwan ma na daban.