Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalt daga shafin yada labarai na Shu’un Arabia cewa, a jiya dubban palastinawa da suka gudanar da sallar Juma’a a birnin Quds sun yi ta rera taken mutuwa ga Al Saud.
Wannan ya biyo bayan ikirarin da masarautar ‘ya’yan aud ta yi ne kan cewa arin masaratar Salman bin abdulaziz ya taka rawa wajen tilasta Isra’ila ta janye koffin lantarki da ta sanya a gaban masallacin Qds.
Al’ummar Palastine sun mayar masada martani ta hanyar yin jerin gwano tare da daga tutoci da kwalaye da aka yi rubutua kansu, da ke cewa mutuwa ga Al Saud, munafukai abokan yahudawa masu cutar da al’ummar musulmi.
Tun kafin wannan lokacin dai Palastinawa suna zargin Al saud da hannu a cikin dukkanin abubuwan da Isra’ila ke yi musu na muzgunawa da cin zalun, inda wannan masarauta ba ta taba nuna damuwa kan cin zarafin da yahudawan Isra’ila suke yi a kan musulmin palastinu ba, maimakon hakan ma, wannan masarauta hankoro take yi domin kula alaka a bayyane ne tsakaninta da Isra’ila, bayan alakar da e tsakaninsu a boye.