Kamfanin dillancin labaran iqn aya bayar da rahoton cewa, bangaren
hulda da jama'a na ciyar yada la'dun muslunci na jamhuriyar muslunci ta Iran ya
bayar da rahoton cewa, ana shirin fara gudanar da wani shiri na bayar da horo
ga malaman kur'ani a Senegal.
Shirin zai gudana ne a garin Tuba babbar cibiyar mabiya darikar Muridiyyah a kasar ta Senegal, a karkashin kulawar cibiyar kula da al'adun muslunci, wanda ofishinta da ke Senegal zai dauki nauyin shirin.
Wannan dais hi ne karon farko da za a gudanar da wannan horo a wajen birnin Dakar wanda cibiyar take daukar nauyinsa, inda Majid Zakilou fitaccen makarancin kur'ani dan kasar Iran zai kasance daga cikin malamai masu bayar da horon.